Living  

Gen Attahiru: Shugaba Buhari Ya Bayyana Dalilinsa Na Rashin Zuwan Jana’izar Tsohon Shugaban Sojoji

Idan ya zamana Babban Hafsan Hafsoshi tare da tawagarsa sun rasu jiya kuma za a yi musu jana’iza yau, ba za a sa ran Shugaban Ƙasa ya halarci wurin taron da ba a tattaro bayan tsaro a kansa ba.”

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana rashin samun rohoton tsaro a matsayin dalilinsa Na rashin halartar jana’izar tsohon shugaban Sojojin Na Kasa, Lt. Gen. Ibrahim Attahiru tare da wasu manyan jami’ai goma (10) da aka gudanar range Asabar da ya gabata.

Attahiru dai ya hadu da ajalinsa ne sanadiyan hadarin jirgin sama a Kaduna ranar juma’ar da ta gabata tare da sauran jami’ai goma.

A kaidance dai fadar shugaban Kasa ta shaida cewa, shugaban kasa na bukatar samun bayanan tsaro Na akalla awa 48 kafin ya samu damar halartar kowace Irin taro da za’ayi a wajen fadan shugaban kasa (villa).

Hadimar Shugaban Ƙasar Kan Sha’anin Soshiyal Midiya, Lauretta Onochie, ta bayyana a shafinta na twita a Litinin cewa, “Kafin Shugaban Kasa ya halarci jana’iza ko wani taro a wajen Fadar Shugaban Ƙasa, wajibi ne a tattara bayanan tsaro game da wurin sa’o’i 48 kafin taron kamar yadda tsarin tsaro ya buƙata.

“Idan ya zamana Babban Hafsan Hafsoshi tare da tawagarsa sun rasu jiya kuma za a yi musu jana’iza yau, ba za a sa ran Shugaban Ƙasa ya halarci wurin taron da ba a tattaro bayan tsaro a kansa ba.”

Ta ci gaba da cewa, “Ba a cim ma mafi ƙarancin sa’o’in 48 da ake buƙata
ba. Game da sha’anin tsaro kuwa, tarurrukan jana’iza wurare ne da manyan
‘yan siyasa kan fuskanci haɗari.

“Sannan batun tsaro da kuma bai
wa Shugaban Ƙasa kariya abu ne da ba a yin sa da son zuciya. Akwai
dokoki da ya zama wajibi a kiyaye su.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *